<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>John Henry Yates, Ira David Sankey</author>
<lyrics>[V1]
 1) Su magauta dayawa ne a kewaye da mu.
 Shaiɗan da dukan runduna sun zo su kā da mu,
 Amma an shirya makamai don wannan yaƙi fa.
 A cikin sunan Yesu ne za mu ci nasara.

[V2]
 KORUS
 Yesu mai nasara, Yesu mai nasara,
 Da sunan Yesu ne mu ke yin nasara.

[V3]
 2) Kwalkwalin ceto bisa kai, ɗamarar gaskiya,
 Da garkuwa ta bangaskiya, sulken adalci ma,
 Shirin bishara takalmanmu ne a ƙafafu,
 Ga takobi na Ruhu ma, wato Maganarsa.
 Korus

[V4]
 3) Mu yi addu'a koyaushe, mu yi aniya fa,
 Mu yi roƙo da naciya don dukan tsarkaka,
 Mu tsaya dai da ƙarfi fa, mu yi tsayayya ma,
 A cikin ikon Yesu ne za mu ci nasara.
 Korus</lyrics>
<title>Su Magauta Dayawa Ne A Kewaye da Mu LW291</title>
<hymn_number>291</hymn_number>
</song>